Al'umma

Darasin Rayuwa Mai “Daci Da Dadi” Da Ya Kamata Mu Sani A Yau

Hoton da ke sama ya nuna wani mutum yana jigilar kowane irin tayoyin mota. Akan hanyar shi, tayar motar shi ta fashe, kuma abin takaici babu tayar da ke yiwa motar daga cikin tayoyin da yake dauke da su.

Yayi zaune cikin takaici

Wannan hoton na musamman shi ne rayuwar wani mutum.

Wannan hoton zai iya zama rayuwar ka, rayuwar ta ko kuma rayuwar shi.

Lokacin da kuka kalli lambobin waya dake ajiye cikin wayar ku, kuna da lambobi masu yawa. Lambobin manyan mutane, abokan hulɗa na ƙananan mutane da abokan hada-hafa na matsakaitan mutane, amma lokacin da kuke buƙatar taimako, za ku gane cewa duk mutanen da kuke da abokan hulɗar su ba su samuwa a wannan lokaci.

A wannan lokacin na fidda rai, idan ka yi waya, ba wanda zai amsa, kuma ’yan kadan da zasu amsa zasu kashe maka wayar a lokacin da suka gane kana bukatar taimako, wasu zasu gaya maka yadda abubuwa suka takure a wajen su, wasu zasu kashe kiran suna iƙirarin sake kiran ku.

Duba lambobin wayoyin

Ka kalli jerin sunayen lambobin da kyau sannan ka ƙidaya adadin mutanen da zasu iya tsayawa a gefen ka a kowane lokaci.

Ku kalli abokai na da’irar ku. Nawa ne daga cikin su zasu iya ɗaukar wannan matakin na kwatsam don ceton ku daga wannan mawuyacin hali ba tare da tunani na biyu ba.

Mutane da yawa sun ci amana da kuma watsi da mutanen da suka fi kauna da kuma amincewa da su.

Misalin wannan hoton sama

Wataƙila wannan hoton yana bada labarin ka/ki ne.

Rayuwar mai zuciyar kirki shine wanda ya kasance yana fifita wasu a gaba da ita.

Rayuwar waccan budurwar da ake yadaura da wasu mata duka da sunan abota amma kuma ka kare da cutar da su.

Rayuwar wannan mutumin da ya kasa jurewa ganin abokinsa yana shan wahala. Dole ne yayi wani abu. Koda ba shi da komai, har yanzu yana ƙoƙari ya nemo hanyar da zai taimaki abokin shi amma duk da haka a ƙarshe, ayyukan shi nagari sun samu sakayya da mugunta.

Gaskiyar rayuwa a yau

Wadannan abubuwan dake sama sune gaskiyar rayuwa a wannan zamani.

Ba duk abokan ka ba ne zasu yi tsalle kan lamarin ka da kuzarin da ka yi amfani da shi don tsalle kan taimakon su ba.