Wasanni

Ɗan Kwallon Da Ya Zura Ƙwallaye 562 A Wasanni 956 Da Ya Buga

An yi la’akari da shi a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan wasan kasar Mexico, Hugo Sanchez ya zura kwallaye 562 a cikin wasanni 956 da ya buga wa kulob da kasa.

Tsohon dan wasan gaban Atletico Madrid da Real Madrid shi ne ke rike da kambun yawan zura kwallo a raga, bayan da ya zura kwallaye masu yawa a tarihin rayuwarsa.

Haka kuma shi ne na 4 da ya fi zura kwallaye a tarihin gasar La Liga sannan kuma shi ne na 7 mafi yawan zura kwallaye a tarihin Real Madrid.