Dan Kwallon Ƙafar Jamus, Robert Bauer Ya Tabbatar Da Musuluntar Shi
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yabawa dan wasan kwallon kafar Jamus Robert Bauer bayan da ya tabbatar da Musulunta a wasu jerin sakonni da ya wallafa a Instagram.
Dan wasan wanda a halin yanzu ya rattaba hannu a kulob din Al-Tai FC na kasar Saudiyya, ya saka hotonsa yana Sallah tare da bayyana cewa ya musulunta ne ta hannun matarsa da danginta.
A cikin labaransa na Instagram, ya kuma rubuta cewa, “Ka shiryar da mu zuwa ga tafarki madaidaici daga Suratul Fatiha,” yayin da wani sakon ya rubuta ayar Al-Qur’ani yana cewa, “kuma yana tare da ku a duk inda kuke.” (Qur’an 57:4).
Bayan ya samu tallafin da ya samu a shafukan sada zumunta, Bauer ya godewa kowa sannan ya bayyana tafiyarsa ta karbar addinin Musulunci.
An haifi Bauer a Jamus a cikin shekarar 1994 ga iyayen Kirista Kazakhstan. Ya hadu da matarsa musulma a Dubai.
“Na ce shahadata shekaru da yawa da suka gabata lokacin da muka yi aure amma ban da masaniya sosai game da hakan,” in ji Bauer a shafinsa na Instagram.
“A tsawon shekaru, na kara koyo amma yanzu, bayan na zo Saudiyya na ji dadin Musulunci kuma na so in sake yin shahada, in karanta Al-Qur’ani da koyo da kuma aiki da shi.
“Ina so in gode muku duka daga cikin zuciyata saboda kauna da goyon baya da nake samu kuma ina jin dadin koyo da girma.”
Dan wasan mai shekaru 28 ya fara aikinsa a Karlsruher SC, kafin ya koma kungiyar Werder Bremen a matakin farko na Bundesliga a shekara ta 2016 sannan kuma a matsayin aro ga FC Nurnberg shekaru biyu bayan haka. Ya kuma buga wasanni lig na Rasha da Belgium kafin ya koma Saudiyya.
Bauer ya buga wa Jamus wasa a gasar cin kofin duniya ta FIFA U-20 na 2015 a New Zealand kuma ya kasance memba a cikin tawagar Jamus da ta lashe lambar azurfa a gasar Olympics ta bazara ta 2016.