Al'umma

Dalilin Da Yasa Shugaban Ƙasa, Tinubu Ya Sauke Wasu Ministoci

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin yada labarai da dabaru Bayo Onanuga ya bayyana dalilin da yasa ya kori Ministoci biyar daga gwamnatin shi.

Onanuga, a wata hira da ya yi da AriseTV a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa an kori ministocin ne a kan muradu na jama’a.

Ya kara da cewa sake fasalin majalisar ministocin ya kasance wani gagarumin aiki kuma wani bangare ne na shirin shugaban kasa tun bayan rantsar da ministocin a bara.

Mataimakin ya tunatar da cewa, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa Hadiza Bala Usman ita ce ta dorawa alhakin kula da aikin tantance ayyukan, wanda ya hada da tattara ra’ayoyin jama’a kan ministocin.

Onanuga ya ce: “Ya gaya musu cewa yana da ikon daukar ma’aikata da kora, kuma ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sauke ministocin da ba za su iya yin aiki ba.

Tinubu ya rubutawa majalisar dattijai don tabbatar da Bianca Ojukwu, Yilwatda, wasu biyar a matsayin ministoci
“Ya kuma bayyana cewa za a yi aikin tantancewar wanda ya ce Hadiza Bala Usman, mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin siyasa ta kamata ta jagoranci.

“Hadiza ta kawo fasaha a wannan aiki, inda ta nemi ‘yan Najeriya su nuna abinda suka sani akan ministoci.

“Don haka, duk wanda aka cire daga cikin Ministoci an cire shi ne bisa hujjar gaskiya. Ra’ayin jama’a na waɗancan ministocin, kuma su ne mutanen da a zahiri suka yi tantamcewar. Shugaban ya yi aiki da sakamakon ne kawai, wato ra’ayin jama’a na wadannan ministocin, abin da ya faru ke nan.”

Jaridar The Nation ta ruwaito a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba, Tinubu ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul, inda ya kori Ministoci kusan biyar, ya kuma nada wasu ministoci 10 tare da nada sabbin ministoci bakwai.