Wasanni

Dalilin Da Yasa Ɗan Wasan Senegal, Krepin Diatta Ya Caccaki Ƴan Afrika

Dan wasan Senegal, Krepin Diatta, ya caccaki jama’a musamman ‘yan Afirka da suka yi mai ba’a a lokacin gasar cin kofin Afirka da ta gabata. Ga abin da ɗan wasan ya fada a shafukan sada zumunta:

“Na ji bakin ciki da na ga wasu ‘yan uwa ‘yan Afirka suna yi mini ba’a, ina yi wa nahiyar mu mai kyau da kauna abu mai kyau, amma ba abin da nake samu sai cin fuska kawai, ba’a ga ‘yan uwana, wannan abu ne mai muni kuma wariyar launin fata ta fito daga can.

Ina bukatan kwarin gwiwar ku ba zagi ba. Na gode wa duk wanda ya ba ni goyon baya. Allah ne kadai yasan karfina kuma ina alfahari da jikina. Ba’ar ku ba za ta canza komai ba a rayuwa ta. Amma abu daya tabbatacce shine ne, dukkan mu ‘yan Afrika ne.” Krepin Diatta ya wallafa.