Al'umma
Dalibai 700 Sun Kammala Karatun Haddar Qur’ani A Habasha
An gudanar da bikin ne a ranar Asabar a wani kauye da ke yankin Oromia na kasar Habasha (Ethiopia).
Duk wadannan dalibai sun yi karatun haddar darussa a wata cibiyar Musulunci mai suna Zaid bin Thabet.
Wani mai wa’azi dan kasar Habasha Sheikh Amin Abreu ya wallafa hotuna da bidiyo a lokacin da yake halartar bikin, inda ya nuna daliban sun yi layi a cikin rigar kauye suna yawo a kan titunan kauyen domin murnar wannan rana.