Al'umma

Bello Turji Ya Nuna Sabbin Kudi, Ya Ce Yana Da Su Fiye Da Miliyan N10 Don Sayen Makamai

Shahararren dan ta’adda ya nuna wasu sabbin takardun kudi na Naira, yana mai ikirarin cewa yana da har N10m ya sayi karin makamai.

An ga wani fitaccen shugaban ‘yan ta’adda mai suna Bello Turji a cikin wani faifan bidiyo da ke nuna wasu sabbin takardun kudi na Naira a cikin karancin kudi.

A cikin wani faifan bidiyo da @Edrees4P ta fitar a shafin Twitter a ranar Laraba 1 ga watan Fabrairu, dan ta’addan wanda ya yi magana da harshen Hausa ya yi ikirarin cewa yana da har naira miliyan 10 daga cikin sabbin kudin naira domin sayen karin makamai.

Rahoton da jaridar Punch ta ruwaito, wasu kafafen yada labarai na tsaro sun ce sabbin takardun naira da ke hannun sa, kudin fansa ne da ake zargin ya karba daga ‘yan uwan ​​wadanda aka sace.

Turji yana daya daga cikin ’yan fashi / ’yan ta’adda 19 da Hedkwatar Tsaro ta ayyana neman su a watan Nuwamba 2022.

Sojojin sun kuma sanya ladan Naira miliyan biyar ga kowannen su.

Wadanda ake nema ruwa a jahohin Katsina, Sokoto da Zamfara.