Wasanni

Antonin Panenka: Ƙwararren Ɗan Wasan Kasar Czech Mai Ritaya

Antonin Panenka ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Czech mai ritaya wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya na kai hare-hare a kungiyoyi kamar Bohemians Prague da Rapid Wien, da kuma tawagar ƙasar Czechoslovakia.

Ya lashe gasar cin kofin nahiyar Turai tare da Czechoslovakia a shekara ta 1976 bayan ya ci bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan karshe da Jamus ta yamma da kwallon da aka yanka a hankali a tsakiyar ragar; salon hukuncin da aka fi sani da panenka.

A shekarar 1980 ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kasar Czechoslovakia kuma kungiyarsa ta zo ta uku a gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar.

A halin yanzu yana da shekaru 73 a duniya.