Wasanni
An Hana Paul Pogba Buga Kwallo Har Tsawon Shekaru Huɗu
Wata Kotun ‘tribunal’ ta yanke wa dan wasan ƙwallon ƙafa Paul Pogba wannan hukuncin ne bayan tabbatar da samun sinadarin “testosterone” a cikin jinin shi bisa dalilin yin amfani da kwayoyin karin kuzari.
Testosterone wani sinadari ne dake ƙarawa mutum juriyar wahala yayin wasanni da abubuwa makamantan su, kamar dambe, wasan tsere, iyo da kwallo.
Ataƙaice dai Pogba ya sha ƙwaya ko kuma anyi masa allurar ƙwaya kafin wasan da aka same shi da wannan laifin a lokacin buga ta.
Sai dai kumaPogba ya musanta shan ƙwayar da aka ce yayi kuma akwai yuwar zai iya daukaka ƙara.
Shan ƙwaya dai ba a dokar musulunci kawai yake haramun ba har da a wasan kwallon kafa da sauran wasanni haramun ne.