An Cire Alkalin Wasa Daga Gasar Cin Kofin Duniya Akan Bayar Da ‘Yellow Cared’ 15 A Wasa Daya
Bayan da aka yi masa suka kan alkalancin wasan da aka yi tsakanin Argentina da Netherlands a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta 2022, an kori alkalin wasa Mateu Lahoz daga gasar, aka kore shi gida.
Bayan wasan, Lionel Messi ya soki Lahoz sosai, kuma Emiliano Martinez, wanda ke taka leda, ya kira shi “mara amfani” kuma ya nuna cewa yana son Netherlands ta yi nasara.
Bayan wasan cizon farce da aka tashi da ci 2-2 bayan karin lokaci, Argentina ta samu nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida inda ta tsallake zuwa zagaye na gaba.
A yayin wasan, Lahoz ya fitar da kati 15 masu ban al’ajabi, wanda yasa manazarta da masu sharhi da dama suka bayyana mamakin dabarun shi na sarrafa wasan.
Bai kamata ya zama abin mamaki ba ganin cewa ba za a bar Lahoz ya sake yin alkalancin wasa a gasar cin kofin duniya ta bana ba, saboda a duk duniya an amince da shi yana da karancin fifiko a tsakanin mahalarta gasar.
A makon nan ne Argentina za ta fafata da Croatia a wasan kusa da na karshe; idan har suka samu nasara, za su kara da wanda ya yi nasara a sauran wasan kusa da na karshe, wanda za a buga tsakanin Faransa da Morocco.