Addini

Addu’ar Tashi Daga Barci

الحمد لله الذي أحيانا بعد ما أماتنا وإليه النشور.

fassara:

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya dauki rayukan mu, kuma zuwa gare shi tashi yake.

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbataa gare shi, ya ce: wanda ya farka da daddare ya ce:

لا إله إلا الله وحده لا شريك له الملك وله الحمد وهوعلى كل شيء قدير. سبحان الله والحمد لله ولا إلهإلا الله والله أكبر ولا حول ولا قوة إلا بالله العليالعظيم، رب اغفر لي.

Fassara:

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi Kadai, babu abokin tarayya a gare Shi; mulki da yabo nasa ne, kuma Shi Mai iko ne bisa komai Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah Shi ne mafi girma, kuma babu
dabara babu karfi sai da Allah, Madaukaki, Mai girma. Ya Ubangijina! Ka gafarta mini.”

Wanda ya fadi wannan za’a gafarta masa, idan kuma yayi addu’a za’a amsa masa, idan kuma ya tashi yayi alwala yayi sallah za’a karbi sallar shi.