1970: Tarihin Shahararren Ɗan Kwallon Brazil Mai Ritaya, Jairzinho Mai Taken (Guguwa)
Jair Ventura Filho, wanda aka fi sani da Jairzinho, ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Brazil mai ritaya wanda ya taka leda a matsayin guguwa.
Wanda ake yi wa lakabi da Hurricane ‘, wato (Guguwa) saboda zura kwallaye masu yawa, ya kasance memba mai mahimmanci kuma wanda ya fi zura kwallaye a tawagar Brazil da ta lashe gasar cin kofin duniya a 1970, inda ya lashe takalmin azurfa a waccan gasa sannan kuma ya zama tauraruwar duniya a waccan shekarar.
Ya buga gasar cin kofin duniya guda uku a jere: 1966, 1970 da 1974 kuma gaba daya ya buga wasanni 81 a duniya, inda ya zura kwallaye 33.
A matakin kulob din, ya taka leda ne a kulob din Botafogo na Brazil inda ya shafe shekaru 12 kuma ya buga wasanni sama da 400. Ya kuma taka leda a kungiyoyi kamar Marseille, Kaizer Chiefs, Cruzeiro da Portuguesa.
Ya cika shekaru 77 a 2021.