Labarai

Ƴan Hisbah Sun Kama Kwamishinan Ayyuka Na Jihar Jigawa Da Matar Aure A Cikin Kango

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Jigawa Auwal Danladi Sankara bisa zargin yin lalata da wata matar aure Tasleem Baba Nabegu.

An kama kwamishinan da Nabegu da hannu a wani gini da bai kammala ba mallakin sa.

A cewar Darakta Janar na Hisbah, Abba Sufi, kamen Sankara ya biyo bayan wasu korafe-korafe da kanin mijin Nabegu ya yi, inda ake zargin kwamishinan yana da hannu a munanan ayyuka.

“Eh, gaskiya ne mun kama Auwal Danladi Sankara, Kwamishinan Jigawa tare da wata matar aure a wani gini da ba a kammala ba nasa.

“Bai sani ba, muna bin sa ne bisa rahotannin da muka samu a kansa,” in ji Sufi.

Nasiru Bulama, mijin Nabegu, ya shigar da kara yana zargin Sankara da yin lalata da matarsa, mahaifiyar ‘ya’yansa biyu.

A cewar shugaban Hisbah, Bulama ya kai rahoton faruwar lamarin ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSS, da hukumar Hisbah.

“Nasiru Bulama ya shigar da karar ne ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano, da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), da hukumar Hisbah, bisa zargin Sankara da hannu wajen lalata da matarsa,” in ji jami’in.