Wasanni

Ɗan Ronaldo Ya Mutu, Yayin Da Ya Fitar Da Bayani Mai Sosa Zuciya

Cristiano Ronaldo ya sanar da mutuwar ɗan shi, bayan da abokin zaman shi wacce suka daɗe tare Georgina Rodriguez ta haifa masa tagwaye maza da tagwaye mata.

Ya rubuta a shafin Instagram a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ma’auratan suka sanyawa hannu: “Abin takaicin mu ne mu sanar ku da cewa yaron mu ya rasu. Shi ne mafi girman zafin da kowane iyaye zai iya ji.

“Haihuwar ƴar mu ne kaɗai ke ba mu ƙarfin rayuwa a wannan lokacin tare da ɗan bege da farin ciki.

Muna so mu gode wa likitoci da ma’aikatan jinya saboda duk kulawar ƙwararru da goyon bayan su. Dukkan mu mun yi baƙin ciki da wannan asarar kuma muna neman sirri a cikin wannan mawuyacin lokaci

“Yaron mu, kai ne abin kaunar mu. Za mu so ka koyaushe.”