Wasanni

Ɗan Kwallon Najeriya Da Ya Taɓa Lashe Kyautar Gwarzon Ɗan Wasan Wata A Gasar Premier League Sau 3

Peter Osaze Odemwingie shi ne dan wasan Najeriya daya tilo da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gasar Premier na wata sau uku (Satumba 2010, Afrilu 2011 da Fabrairu 2012)- duk a West Brom, inda ya ci kwallaye 30 a gasar Premier.

A matakin kasa da kasa, ya buga wa Najeriya wasanni 63 ya kuma ci kwallaye 10. Ya buga gasar AFCON hudu da kuma gasar cin kofin duniya guda biyu.

Ya zura kwallo a ragar Angola a kwallon shi ta farko a duniya a wasan neman tikitin shiga gasar AFCON a 2004, sannan ya zura a ragar Afirka ta Kudu kwallaye biyu masu ban sha’awa a gasar yadda ya kamata.

A shekarar 2014, Odemwingie ya zura kwallo daya tilo a wasan inda Najeriya ta doke Bosnia da ci 1-0, abin da ya baiwa Super Eagles damar lashe kofin duniya na farko tun shekarar 1998.

Bayan West Brom, ya buga wasa a kungiyoyi irin su Bendel Insurance (inda ya fara aikinsa), La Louviere, Lille, Lokomotiv Moscow da Stoke City. A karshe ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Madura United ta kasar Indonesiya sannan ya yi ritaya a shekarar 2018.