Wasanni

Ɗan Kwallon Da Ya Zura Ƙwalleye Fiye Da 300, Kuma Bai Taɓa Samun Jan Kati Ba

Hernan Crespo ya ci wa Argentina kwallaye 35 a wasanni 64 da ya buga, kuma shine dan wasan kasar na 4 da ya fi zura kwallaye a bayan Aguero da Batistuta da kuma Messi.

A matakin kulob din, ya buga wa kungiyoyi irinsu River Plate da Parma da Lazio da Inter Milan da Chelsea da AC Milan, inda ya lashe kofin Premier da Seria A da UEFA da dai sauransu.

Ya zama dan wasa mafi tsada a duniya lokacin da Lazio ta dauko shi daga Parma a 2000 kan Yuro miliyan 56.

Crespo ya zura kwallaye sama da 300 a cikin aikin da ya shafe shekaru 19 kuma bai taba samun jan kati ba.