Wasanni

Ɗan Kwallon Da Ya Share Fiye Da Minti 75 Baya Numfashi Bayan Ya Samu Bugun Zuciya A Filin Wasa

Komawa baya s cikin shekarsr 2012, yayin wasan cin kofin FA tsakanin Bolton Wanderers da Tottenham Hotspur a White Hart Lane, dan wasan tsakiyar Bolton mai shekaru 23 Fabrice Muamba ya kamu da bugun zuciya kuma ya fadi a filin wasa kuma aka daina wasan.

An bayyana cewa zuciyar Muamba ta daina bugawa har na tsawon mintuna 78 amma likitocin sun samu damar shawo kan lamarin kuma ya samu sauki.

Bayan shawarwarin likita, Muamba ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo a watan Agustan 2012, yana da shekaru 24 kacal.

Daga baya ya tattauna da Dr Jonathan Tobin, wanda shi ne likitan tawagar Bolton Wanderers a lokacin da lamarin ya faru.

Muamba: Likita, ka san lokacin da nake asibiti, ka yi tunanin da zan farka?

Tobin: A’a, ban yi tsammanin za ka sake tashi ba, domin babu wanda yayi hakan.

Muamba: Da gaske kake?

Tobin: Ba wanda ya yi tunanin za ka farka. Ka mutu tsawon mintuna 78.

Advertisement