Al'umma

Wani Ɗan China Da Ya Kashe Budurwar Shi A Kano, Ya Tona Babban Sirrin Miliyan N60

Kamar yadda muka samu daga Vanguard da wasu majiyoyi masu sahihanci, ya kamata a tuna cewa a wani lokaci a shekarar da ta gabata ne aka kama wani dan kasar China mai suna Frank Creg-Quangrong da laifin dabawa masoyiyar shi yar Najeriya mai suna Ummukulsum Sani wuka har lahira. Rasuwar Ummukulsum ta haifar da martani da yawa a shafukan sada zumunta.

Bayanan da aka samu daga wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Janairu, dan kasar China ya yi wani abin mamaki a babbar kotun jihar Kano. Ya bayyana cewa ya kashe mata sama da Naira miliyan N60 kafin ya kashe ta. Frank Creg-Quangrong wanda dan kasuwa ne na duniya, Musulmi, kuma yana zaune a Kano ya bayyana cewa a shekarar 2020, marigayiyar masoyiyar shi ta samu tuntubar shi daga wajen kawarta kuma ta shaida mai cewa tana son shi kuma tana son auren shi.

Ya ce sun ce dangantakar su a watan Yulin 2020 kuma ta fara neman kudi. Ya ba ta akan tana so. Ya ce, “Na tura sama da Naira miliyan N60 zuwa asusun ajiyar ta na banki, Naira miliyan N18 don fara kasuwanci, gidan Naira miliyan N4, da kuma Naira miliyan N6 na ilimin Jami’a da dai sauran su, duk lokacin da na je na dauke ta don cin abinci a gida mahaifiyar ta kullum barka da zuwa ake min.”

Ya bayyana cewa ya yi matukar kaduwa da ya gano a shekarar 2022 cewa Ummukulsum Sani, masoyiyar shi marigayiya ta auri wani. Ya ce, “Na ji takaici da takaici don haka na koma Abuja, ta ci gaba da kira na tana hira da ni a WhatsApp, ta ci gaba da neman kudi, daga baya ta ce min ta rabu da shi, ta ce in dawo wurin ta kuma ta yi alkawarin aure na karo na biyu.”

Ya bayyana wa kotun cewa a ranar 13 ga Satumba 2022, ta nemi kudi domin ta kammala aikin ginin ta a Abuja. Yace mata bashi da kud’in ta fusata ta daina d’aukar kiran shi.

Advertisement