Labarai

Ƙasar Somalia Ta Haramta TikTok Da Telegram Akan Rashin Tsaro

A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin Somaliya ta haramta amfani da dandalin sada zumunta na TikTok da Telegram a fadin kasar.

Gwamnatin ta kuma haramta amfani da manhajar yin caca ta yanar gizo kan zargin amfani da hanyoyin da ‘yan ta’adda ke yi wajen yada farfaganda.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar sadarwa da fasaha ta kasar ta fitar, gwamnati ta umarci masu samar da intanet da su aiwatar da dokar nan da ranar 24 ga watan Agusta ko kuma su fuskanci shari’a.

Ana sa ran gwamnatin kasar za ta sake kai wani farmaki kan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Kungiyar da ke da alaka da Al-Qaeda ta kwashe fiye da shekaru 15 tana tada kayar baya a kan gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a kasar da ke yankin kahon Afirka.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A wani yunkuri na gaggauta yaki da kuma kawar da ‘yan ta’adda da suka zubar da jinin al’ummar Somaliya, ministan sadarwa da fasaha ya umurci kamfanonin da ke samar da ayyukan intanet da su dakatar da aikace-aikacen yin fare na TikTok, Telegram, da 1XBET. wadanda ‘yan ta’adda da kungiyoyin da ke da alhakin yada lalata suke amfani da su wajen yada hotuna, hotuna da kuma yaudarar al’umma.”