Labarai

Wata Ɗaya Bayan Nijar, Sojoji Sun Ƙwace Mulki A Kasar Gabon

Wata guda bayan da sojoji a Jamhuriyar Nijar suka hambarar da zababben shugaban kasar ta hanyar juyin mulki, takwaransu na kasar Gabon ya sanar a gidan talabijin cewa sun soke zaben kasar tare da kwace mulki.

Da juyin mulkin da aka yi a Gabon, a halin yanzu kasashen Afirka bakwai na karkashin mulkin soja: Chadi, Nijar, Burkina Faso, Guinea, Sudan da Mali.

Juyin mulkin da aka yi a Gabon ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke shirin kada kuri’a a babban zaben kasar da aka gudanar a ranar 26 ga watan Agusta.

Jami’an sojan da aka bayyana a matsayin CTRI (Kwamitin mika mulki da maido da cibiyoyi), jami’an soji sun dora aikinsu ne a kan munanan rikice-rikicen siyasa da suka dabaibaye kasar nan saboda rashin gaskiya.

“A yau, kasarmu tana cikin wani mummunan rikicin siyasa, sakamakon rashin rikon amana, mulkin da ba a taba tsammani ba wanda ya haifar da durkushewar hadin kan al’umma wanda ke jefa kasar cikin rudani.

“Don haka, mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ke kan mulki”, in ji su.

Juyin mulkin dai ya kawo karshen mulkin shugaba Ali Bongo, wanda ke kan mulki tun shekara ta 2009 lokacin da ya gaji mahaifinsa Omar Bongo.

Hukumomin zaben Gabon sun ayyana Bongo wanda ke neman wa’adi na uku a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 64 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben na ranar Asabar.

Hakazalika rundunar sojin ta sanar da rufe kan iyakar har zuwa lokacin da za a sanar da cewa ta rusa dukkanin hukumomin gwamnati da suka hada da majalisar dokoki da hukumar zabe da kotun tsarin mulki da kuma fadar shugaban kasa.

Sai dai matsalar ta fara ne a lokacin da ‘yan adawa da sojoji suka ki amincewa da sakamakon da aka bayyana bisa hujjar cewa an yi amfani da wannan adadi.