Labarai

Wasu Matsafa Sun Cire Idon Wani Almajiri Dalibin Islamiyya A Bauchi

Wasu mutane biyu da har yanzu ba a tantance ba a garin Kafin Madaki hedikwatar karamar hukumar Ganjuwa a jihar Bauchi, sun cire idon wani dalibi dan shekara 12 da haihuwa.

PUNCH Metro ta tattaro cewa wanda lamarin ya shafa, Najib Hussaini, dan asalin jihar Kano, ya zo Kafin Madaki ne domin samun karatun Al-Qur’ani.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Yace kwamishinan ‘yan sandan jihar Aminu Alhassan ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, inda ya ce an fara farautar wadanda ake zargin.

Kanun labaran ya janyo cece-ku-ce a tsakanin masu amfani da shafin Facebook, Karanta wasu daga cikin martanin ‘yan Najeriya da suka ci karo da kanun labarai a Facebook:

Source: Jaridar Punch da Facebook