Labarai

Wani Mutum Ya Kashe Kansa A Jihar Adamawa Bayan An Zarge Shi Da Laifin Satar ₦40,000

Wani matashi mai shekaru 34 mai suna Iliya Adamu ya rataye kan shi bayan an zarge shi da satar naira ₦40,000 na dan uwan shi a jihar Adamawa, kamar yadda SaharaReporters ta gano.

An gano gawar Adamu a ranar Talata rataye a kan shi wata bishiya a wani daji da ke kusa da Girei a karamar hukumar Girei ta jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa Adamu ya kashe kan shi ne saboda ya kasa jurewa ana yi masa izgili da kiran barawo. An ce dan uwan shi ya nuna mai yatsa ne a cikin bacewar ₦40,000 da aka ajiye a gidan su.

Bayan ya sha musanta zargin satar kudin, Adamu ya yanke shawarar kashe kan shi don ya kawar da kunya.

An samun mugun labari bayan ganin gawar shi da aka same shi a rataye a jikin bishiya, a safiyar Talata, bayan ya bace kwana biyu.

Majiyoyi sun ce an gano gwanho na kashe kwari a karkashin bishiyar inda gawar shi ta ke rataye.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace, ‘’Yan sandan na binciken dan kunar bakin wake.