Labarai

Wane Ne Omar Tchiani, Da Ake Zargi Da Kitsa Juyin Mulki A Nijar

Bayan saukar shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum daga kan karagar mulki a ranar Laraba, Janar Omar Tchiani, kwamandan masu tsaron fadar shugaban kasa, rahotannin cikin gida da dama sun bayyana shi a matsayin wanda yayi juyin mulki.

Da sanyin safiyar Larabar ne mambobi na sashe na musamman karkashin jagorancin Tchiani suka tsare Bazoum a cikin fadar shugaban kasa, lamarin da ya sa shugabannin yankin suka shirya shirin shiga tsakani cikin gaggawa don kokarin hana juyin mulki.

Sa’o’i kadan bayan haka, wasu gungun sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Afirka ta Yamma suna ikirarin cewa sun karbi ragamar shugabancin kasar.

“Jami’an tsaron sun yanke shawarar kawo karshen mulkin da kuka saba da shi,” in ji Kanar-Manjo Amadou Abdramane a cikin wata sanarwa da aka watsa a gidan talabijin na kasa, tare da wasu mutane tara sanye da kakin, wani bangare na kungiyar da ke kiran ita kanta Majalisar Tsaro ta Kasa.

Abdramane ya kuma ce an dakatar da dukkan cibiyoyi, an rufe iyakokin kasa da na sama kuma an kafa dokar hana fita.

Duk da yake Tchiani baya halarta a gidan talabijin ba, ana ganin shi yana da matukar tasiri a bayan fage a cikin abubuwan da suka faru a ranar Laraba.

Tun a shekarar 2015 ya ke jagorantar dakarun tsaron fadar shugaban kasar, kuma ya kasance na hannun damar tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou – dan siyasar da ya jagoranci kasar har zuwa shekarar 2021.

Wani abin mamaki shi ne, shi ne ya jagoranci rundunar da ta dakile yunkurin juyin mulki a kasar a watan Maris din shekarar 2021, lokacin da wata runduna ta soji ta yi kokarin kwace fadar shugaban kasar kwanaki kadan kafin a rantsar da Bazoum da aka zaba.

Zaben Bazoum shi ne karon farko da Nijar ta mika mulki cikin lumana da dimokuradiyya tun bayan da ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960. Da ya hau kan karagar mulki, ya rike Janar din a matsayin shugaban masu tsaron fadar shugaban kasa, wani bangare na musamman mai dauke da sojoji kusan 2,000.

Ba a fayyace dalilan da suka sa Tchiani ya jagoranci juyin mulkin ba amma akwai jita-jitar cewa hambararren shugaban ya so ya sallame shi kwanaki kadan da suka gabata, Paul Melly, masani a Nijar a cibiyar bincike ta Chatham House da ke Landan, ya shaida wa Al Jazeera.

Akwai kuma rade-radin cewa hakan na iya kasancewa saboda shekarun Janar din, wanda ke da shekaru 62, ko kuma ake zargin rashin gamsuwa da wasu daga cikin sojojin da suka hada da na masu tsaron fadar shugaban kasa.

Arewa Times ba ta iya tabbatar da waɗannan hasashe da kanta ba.