Labarai

WAEC Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2023

Hukumar shirya jarrabawar Afrika ta Yamma (WAEC) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka ta 2023 (WASSCE).

Hukumar jarrabawar ta fitar da sakamakon ne a ranar Litinin.

Patrick Areghan, shugaban ofishin Najeriya (HNO) na WAEC, ya ce daga cikin mutane 1,613,733 da suka zana jarrabawar, an hana sakamakon ‘yan takara 262,803 “saboda rahotannin da aka samu na rashin gudanar da jarabawar.”

Ya ce an samu ci gaba a fannin samun gurbin karatu a matsayin jimillan mutane 1,361,608, masu wakiltar kashi 84.38 cikin 100, sun samu kiredit da sama da haka a mafi karancin darussa biyar masu dauke da harshen Ingilishi ko lissafi.

Haka kuma, ’yan takara 1,287,920, wadanda ke wakiltar kashi 79.81 cikin 100 na jimlar ’yan takarar, sun samu kiredit da sama da haka a cikin mafi karancin darussa biyar, da suka hada da Ingilishi da Lissafi.