Al'umma

Tarihin Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan

An Haifi Farfesa Abdullahi Saleh Usma  Pakistan a Shekara ta 1957 a Karamar Hukumar Mai Adua dake Jihar Katsina, Najeriya.

Saleh Pakistan ya fara karatun shi a wajen mahaifin shi, daga Bisani ya ci gaba a wajen kakan shi Mallam Usman A Garin Gwiwa dake Jihar Jigawa. Daga Bisani ya dawo a Jihar Kano inda anan ne ya samu nasarar kammala Haddar Al-kur’anin mai girma yana kimanin shekara (17) a duniya.

Pakistan yayi makarantar koyar da harshen Larabci ta Jihar Kano, wato S.A.S KANO. Daga nan kuma Pakistan yayi tazarce zuwa Jami’ar Musulunci ta Madina inda acan ne ya kammala Degree din sshi na farko kuma ya zauna shida Iyalan shi a can ƙasar Saudiyya.

Bugu da kari, Pakistan ya samu ci gaban karatun shi a kasar Pakistan inda a  can ne yayi Masters din shi, sannan ya ci gaba da ayyuka na Da’awa da Karantarwa na tsawon lokaci, kuma anan ne Allah ya al-barkace shi da samun karuwa.

Daga nan Pakistan ya zarto zuwa Gida Najeriya Inda ya shiga Jami’ar dan Fodio inda anan ne ya samu damar kammala (P.H.D) din shi.

Yanzu kuma ya zama Farfesa a Jami’ar Al-Qalam University dake Katsina.

Babban Malami Saleh Pakistan a yanzu dai shine Shugaban Kwamitin Masallatai na kungiyar Izala, JIBWIS ta kasa kuma shugabanta na Jihar Kano. Sannan shine B’babban Limami na Masallacin Sheik Ja’afar Mahmud Adam dake Unguwar Tudun Murtala a Kano. Kuma babban jagora na Makarantar Musulunci ta MANARU dake Unguwar Tudun Murtalan a Birinin Kano.

Farfesa Pakistan ya sadaukar da rayuwar shi cikin ayyuka na kira izuwa ga addinin Musulunci.

Wannan shine tarihin Mallam a takaice.