Labarai

Sama Da Mutane 80 Sun Mutu Bayan Jirgin Ruwa Ya Nutse A Congo

Fiye da mutane 80 ne suka mutu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) bayan da jirgin ruwan da suke tafiya ya nutse, kamar yadda shugaban kasar Felix Tshisekedi ya sanar.

Hatsarin ya afku ne a ranar Laraba a kogin Kwa, kimanin kilomita 70 (mil 43) daga birnin Mushie na lardin Mai-Ndombe.

“Shugaban kasar yana kira da a gudanar da bincike kan hakikanin musabbabin wannan mummunan lamari, don hana irin wannan bala’i sake afkuwa a nan gaba,” in ji fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa da aka buga akan X.

Tshisekedi “ya aika ta’aziyya ga iyalai da kuma masoyan wadanda abin ya shafa,” in ji sanarwar, ta kara da cewa ya umurci hukumomi da su dauki matakai tare da taimakawa wadanda abin ya shafa.

Rita Bola Dula, gwamnan lardin Mai-Ndombe, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa lamarin ya faru ne sakamakon tukin dare.

Mummunan hadurran kwale-kwale na zama ruwan dare a DRC, inda ake yawan lodin jiragen ruwa fiye da karfinsu. Ƙasar tsakiyar Afirka tana da ƙananan titunan kwalta a fadin ƙasarta da ke da dazuzzuka, kuma tafiye-tafiyen kogi ya zama ruwan dare.

Advertisement