Labarai

Sabbin Ƴan Ta’adda, Lakurawa Sun Kashe Mutane 15 A Jihar Kebbi

Rikicin da ya barke tsakanin al’ummar Mera da sabuwar kungiyar ta’addanci, Lakurawa, ya yi sanadin mutuwar mutane 15 a jihar Kebbi.

Ana zargin sabuwar kungiyar da ake kira Lakurawa da alaka da kungiyar ISIS da ke aiki a yankin Sahel.

Rahoton BBC Hausa ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a kusa da unguwar Mera da ke karamar hukumar Augie a jihar Kebbi.

Rikicin, kamar yadda wata majiya da ta zanta da BBC Hausa ta bayyana, ya samo asali ne a lokacin da ‘yan kungiyar ta’adda ta Lakurawa suka ci karo da wani makiyayi da ke yankin suka yi yunkurin sace masa dabbobi.

Makiyayin dai, kamar yadda rahotanni suka bayyana, ya garzaya zuwa wurin al’ummar garin, inda ya yi ta ihu, lamarin da ya sa al’ummar yankin suka yi tattaki zuwa inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan da ya kai ga halaka mutane 15, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

“Mutanen yankin sun yi nasarar kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan tare da raunata wasu. Wadanda suka tsira daga cikin ‘yan ta’addan suka tafi da su.”

“Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Umar Abubakar Tafida, ya kai ziyarar ta’aziyya ga mutanen Mera, tare da rakiyar Kwamishinan ‘yan sanda da Sarkin Argungu.”

Advertisement