Mutumin Nan Mai Zanen Batanci Ga Annabi S.A.W, Kurt Westergaard Ya Mutu
Shahararren mai zane-zanen batanci Annabi Muhammad “tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi” dan kasar Denmark Kurt Westergaard, wanda ya tayar da hankali a duniyar Musulmi, ya mutu yana da shekara 86.
Westergaard ya mutu a cikin barcinsa bayan doguwar rashin lafiya, kamar yadda danginsa suka shaida wa jaridar Berlingske ta Denmark ranar Lahadi.
Musulmai suna girmama annabi Muhammadu kuma kowane irin zane na gani haramtacce ne a musulunce.
Ba a fara ganin katunan majigin ba tun da farko, amma bayan makonni biyu, an gudanar da zanga-zangar adawa da su a Copenhagen sannan kuma jakadu daga kasashen Musulmi a Denmark sun gabatar da zanga-zangar.
Daga nan fushin ya rikide zuwa zanga-zangar kin jinin Denmark a duk fadin duniyar Musulmi a watan Fabrairun 2006. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun zama masu tashin hankali. An kai hari kan ofisoshin jakadancin Denmark da na Norway kuma mutane da dama sun mutu.
Abubuwan da suka faru sun haifar da muhawara game da ƙyamar Islama da iyakokin ‘yancin faɗar albarkacin baki da addini a Denmark da ma wasu wurare.
A shekarar 2015, an kashe mutane 12 a wani hari da aka kai a Charlie Hebdo mako-mako a Paris, wanda ya sake buga zane-zanen a 2012.
Westergaard yana aiki a Jyllands-Posten tun a tsakiyar shekarun 1980 a matsayin mai zane kuma a cewar Berlingske an buga zanen da ake magana sau daya a baya amma ba tare da haifar da wata takaddama ba.
A cikin shekarun karshe na rayuwarsa Westergaard, kamar sauran mutane da ke da alaƙa da zane-zanen, dole ne su zauna cikin tsaron ‘yan sanda a wani wurin sirri.
A farkon shekarar 2010, ‘yan sandan Denmark sun cafke wani mutum mai shekaru 28 dauke da wuka a gidan Westergaard, inda yake shirin kashe shi.