Mutumin Da Aka Kashe A Sakkwato Bai Zagi Annabi S.A.W Ba
Zancen gaskiya game da wannan mutumin da aka kashe yau a Sakkwato da sunan ya zagi fiyayyan halitta Annabi S.A.W.
Gardamar Aqida ce ta kaure a tsakanin su, sunan mutumin da aka kashe Mallam Usman, Gardama ce ta kaure a tsakanin su akan nema ko rashin neman taimakon Annabi Muhammad (S.A.W). Suna cikin gardamar sai wani yace masa kada ya sake fadin ba’a neman taimako a wurin Annabi S.A.W sai shi kuma ya sake fadi, nan take suka fara mishi ihun ya zagi fiyayyan halitta, duka da sauran su wanda hakan ya zamo sanadin rayuwar shi.
Wannan shine zancen gaskiya da aka mini bayani ta bangarori da dama. A lokacin da kashe matashin duk Duniya ta dauka cewa lallai ya aikata hakan sai daga baya aka bayyana ainahin gaskiyar abunda ya faru, rikici ne na Aqida, hisabi kuma sai a wurin Ubangiji.
Rikicin Aqidah babu irin abunda bai jawowa, har fadan kasa da kasa yana hadawa, yana daga cikin dalilan da yasa duk wani abu da ya shafi Aqida ban cewa komai, domin ni ba malami bane ni dalibi ne.
Allah muna rokon ka da ka kara hada kawunan mu wuri guda, ka bamu ikon bin gaskiya komin dacin ta, Yaa Hayyu Yaa Qayyum.
Comr Abba Sani Pantami…