Kasuwanci

Mene Ne Kayayyakin Dijital?

Ya zamu yi muyi bayani game da abinda ake cewa kayayyakin dijital a wannan zamani.

Mene ne kayayyakin dijital, kuma me ye dalilin da yasa zaka zaɓe su?

Kayayyakin Dijital: Kaya ne da suke a yanar gizo irin su Ebooks, Online Courses, waƙoƙi, fina-finai da dai duk wani abu da yake a internet kuma za’a iya samun wani da shi a wasu lokutan shi ake kira Digital Products.

Ba kamar physical ba ne, kayayyakin dijital ana iya sayar dasu cikin sauki kuma ana samun su a wannan lokaci da in aka siya babu jira.

Yawan yadda mutane suke ci gaba da internet hakan yana bada dama ga masu kasuwancin intanet suna samu suna ci gaba da sayar da kayan su a yanar gizo.

Ɗaya daga cikin amfanin sayar da shi ne babu maganar girman abin. Ba kamar ba kamar kayayyakin da muke gani a fili ba ne wanda dole sai sun bukaci karin kayan aiki kamin akara yawan su kayan sannan a sayar dasu.

Ana iya canza kayayyakin yanar gizo sannan a sayar da shi babu maganar karewar sa zaka riƙa sayar da shi ba tare da ka karawa kayayyakin na ka kudi ba.

Hakan yana nufin zaka iya samun yan canji “KUDADE” ba tare da ka sha wahala irin wanda zaka sha wajen sayar da a fili ba ba.