Labarai

Matashi Ya Jefa Mahaifin Shi Cikin Rijiya Kan Rikicin Fili

Wani matashi ya jefa mahaifinsa a cikin rijiya a lokacin da ake rikicin fili.

Mutumin mai shekaru 60 a duniya yanzu haka yana fafutukar rayuwarsa a wata asibitin Kenya bayan ya shafe kwanaki uku a cikin rijiyar mai kafa 20 da dansa ya jefa shi a ciki.

Samuel Tanui daga yankin Emitiot da ke yankin Chepalungu da ke gundumar Bomet a kasar Kenya, dan nasa ne ya jefa shi cikin rijiyar sakamakon rikicin fili.

A cewar mataimakin shugaban yankin Cif Lenny Ngeno, tun da farko Tanui ya ki bai wa dansa mai shekaru 22 Charles Kiplangat Rotich izinin sayar da fili ga iyalan kuma ana kyautata zaton hakan ne ya sa dan nasa ya kitsa wani shiri na kashe shi.

Bayan jefa shi cikin rijiya, Rotich ya ci gaba da harkokinsa na yau da kullum yana tunanin mahaifinsa ya rasu.

Dattijon ya yi nasarar yin kuka sosai don wasu masu wucewa su ji shi kuma a lokacin ne aka ceto shi. Daga nan aka garzaya da shi asibiti.