Labarai

Masar Ta Hana Ƴan Kasashen Waje Fita Daga Gaza Ta Iyakar Ta Sai An Cika Sharadi

Hukumomin Masar sun ki barin Amurkawa da wasu ‘yan kasashen waje shiga cikin kasar Masar ta kan iyakar Rafah a ranar Asabar.

Hukumomin kasar sun dage kan cewa dole ne mashigar kan iyakar ta saukaka shigar da kayayyakin jin kai zuwa Gaza, kamar yadda kafar yada labaran kasar Masar ta AlQahera ta ruwaito.

Tashar yada labarai ta AlQahera ta bayar da rahoton cewa, “Hukumomin Masar sun yi watsi da ra’ayin yin amfani da mashigar kan iyakar Rafah don fitar da baki daga Gaza.”

Tashar ta nakalto majiyar Masar tana cewa, “Matsayin Masar a bayyane yake, kuma yana bukatar samar da saukin shiga da shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza.”

Falasdinawa-Amurkawa suna jiran bude hanyar kan iyakar Rafah tsakanin zirin Gaza da Masar a ranar Asabar, bayan da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta aike da umarni ga iyalansu a ranar Juma’a tana gaya musu cewa “mai yiwuwa a bude mashigar” da yammacin ranar Asabar.