Labarai

Lokacin Kafa Tarihi Yayi – Inji Roberto Mancini Akan Mukaminsa Na Sabon Koci

Tsohon kocin Manchester City, Roberto Mancini ya ce yana sha’awar kafa tarihi bayan an nada shi sabon kocin tawagar kwallon kafar Saudiyya.

Mancini ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu na kusan Yuro miliyan 30 a duk kakar ranar Lahadi.

Hakan na zuwa ne kasa da ‘yan makonni bayan ya yi murabus daga mukaminsa na kocin tawagar kwallon kafar Italiya.

Da yake mayar da martani game da sabon nadin nasa, Mancini ya ce a cikin wani faifan bidiyo da aka buga a dandalin sada zumunta na X, wanda a da ake kira Twitter: “Na kafa tarihi a Turai, yanzu lokaci ya yi da zan kafa tarihi da Saudiyya.”

Dan Italiyan ya kara da cewa a shafinsa na Twitter: “Na gode wa Shugaba Yasser Al Misehal.

“Na yi farin ciki da na amince da wannan sabon aikin wanda ya ta’allaka ne kan raba dabarun ci gaba a fagen kwallon kafa musamman a duniyar matasa da nake damu da su.

“Wannan aikin shine sanin darajar da aka danganta ga ƙwallon ƙafa na Italiya kuma a cikin wannan gogewa zan yi alfahari da kawo ruhun Italiyanci ga duniya.”