Kasuwanci

Litar Fetur Za Ta Koma N700 A Najeriya – ‘Yan Kasuwa

‘Yan kasuwar dake harkar fetur na hasashen cewa da yiwuwar cewa farashin litar man fetur ta kai N700 a arewacin Najeriya, farawa daga watan Juli mai kamawa na da yan kwanaki.

Wani jigo a kungiyar dillalai da masu safarar man fetur din Mike Osatuyi ya ce a kudancin Najeriya, farashin litar man na iya haura N700 madamar suka fara shigo da man da kan su daga watan Juli.