Labarai

Kotu Ta Yanke Wa Zakara Hukuncin Kisa Bisa Laifin Ta Da Zaune Tsaye

Wata Kotun Majistare da ke Gidan Murtala a Jihar Kano, ta umurci wani mutum da ya yanka zakaran shi (kaza) bisa zarginsa da tada zaune tsaye a unguwar da yake zaune.

Arewa Times Hausa ta samu cewa wani makwabci mai suna Yusuf Muhammad Ja’en ya shigar da kara a kotun, inda ya yi korafin cewa zakaran Isyaku Shu’aibu ya hana unguwar hutun da ya dace, wanda hakan ba zai haifar da da mai ido a koda yaushe.

Ja’en ya yi zargin cewa zakaran yana cara da yawa, bai ba su kwanciyar hankali. Da ta ji ta bakin bangarorin biyu a zaman da suka yi a ranar Talata, Alkalin Kotun, Halima Wali, ta baiwa Yusuf har zuwa ranar Juma’a da ya yanka zakaran.

Sai dai rahotanni sun ce Shu’aibu ya shaida wa kotun cewa ya siyo tsuntsun ne domin murnar Juma’a, sannan ya roki kotun da ta ba shi damar ci gaba da rike shi har zuwa ranar Kirsimeti kafin ya yanka shi domin bikin iyali.

Alkali Wali ta yi kunnen uwar shegu da rokon, amma ta gargade shi da cewa kada ku bari tsuntsayen su rika yawo a yankin da hargitsa mazauna yankin.

Ta kuma bukaci ya tabbatar ya yanka tsuntsun a ranar Juma’a kamar yadda ya yi alkawari ko kuma ya fuskanci hukunci daga kotu.