Kasuwanci

Kamfanin NNPC Ya Sake Ƙara Ƙudin Man Fetur

Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC, ya sake ƙara farashin man fetur na Premium Motor Spirit, PMS, wanda aka fi sani da man fetur zuwa N1,030 kowace lita.

Wakilin Daily Post ya lura da wannan karin kudin a wasu gidajen man NNPC da ke Abuja ranar Laraba.

Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan da hukumar ta NNPC ta yanke shawarar soke yarjejeniyar saye mai daga matatar man Dangote.

Wannan yana nufin NNPC ba za ta ƙara zama ita kaɗai ba, kuma yan kasuwa yanzu za su iya tattaunawa kan farashin kai tsaye da matatar Dangote.

A babban birnin tarayya, FCT, a baya ana siyar da kayan a kan Naira 897 kan kowace lita.

Wakilin Daily Post ya kara da cewa, a Legas, man da a da ake sayar da shi kan Naira 885 kan kowace lita, yanzu ana sayar da shi kan Naira 998 a cikin dogayen layukan da ake yi.