Kasuwanci

Jerin Sunayen Jihohin Da Ake Hako Danyen Mai A Arewacin Najeriya

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, kamfanin NNPC ya sha bayyana muradin shi na gano mai a wasu sassan kasar nan baya ga jihohin Neja Delta.

A cikin ayyukanta na aikin hako man fetur, NNPC ta kebe jihohin da ake sa ran za a gano mai da suka hada da Neja, Nasarawa, Sokoto, Borno, Yobe, Adamawa, Bauchi, da Gombe.

Ya zuwa yanzu dai jihohin Bauchi, Gombe, Nassarawa, da Kogi ne kawai aka samu nasarar gano mai a arewacin kasar.

A shekarar 2022, jihar Kogi ta samu rabon rarar man fetur na farko a matsayin jiha mai hako man fetur, wanda hakan ya sa ta zama jihar arewa ta farko da ta samu irin wannan gata a kasar.

Yayin da aka fara hakar danyen mai a filin Kolmani da ke kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe.