Nishaɗi

Jarumin KannyWood, Sulaiman Alaqa Ya Rasu

Allah ya yiwa Sulaiman Alaqa, jarumi a masana’antar film ta Kannywood rasuwa.

Kamar yadda Arewa Times Hausa ta samu labari, jarumin ya rasu ne a ranar Litinin (yau, 22-7-2024), bayan yayi fama da wata gajeriyar rashin lafiya da ba’a bayyana ba.

Haka zalika, tuni aka yi jana’izar shi a gidan su dake unguwar Gwammaja, cikin jihar Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.