Labarai

Jarumin KannyWood, Kawu Mala Ya Rasu

Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood da ke shirya fina-finai a cikin harshen Hausa a arewacin Najeriya, na jimamin rashin daya daga cikin mambobinta, Aminu Muhammad, wanda aka fi sani da Kawu Mala a cikin shirin ‘Dadin Kowa’ da ake yadawa a gidan talabijin na Arewa24.

Bayan yasha fama da ciwon zuciya na tsawon shekaru da dama, jarumin ya rasu a yammacin ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu. Mala ya kasance fitaccen jarumin da ya shafe shekaru 20 yana gogewa, kuma ya samu karbuwa sosai a cikin fitattun shirye-shiryen talabijin.

Mala, ya bar matarsa ​​da ‘ya’ya sama da 10, an yi jana’izar sa ne a safiyar ranar Litinin a makabartar Haye da ke karamar hukumar Nasarawa a Jihar Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Advertisement