Labarai

Hambararren Shugaban Kasar Gabon Ya Roki Abokai Su Yi Magana Kan Juyin Mulki

Wani faifan bidiyo na hambararren shugaban Gabon Ali Bongo yana kira ga “abokansa” da su tofa albarkacin bakinsu bayan nasarar juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar mai arzikin man fetur a tsakiyar Afirka ya bayyana.

Bongo a cikin faifan bidiyon ya nemi abokansa da su “yi hayaniya” game da mutanen da suka kama shi da iyalinsa.

Ya ce, “Ina aika sako ga duk abokai da muke da su a duk faɗin duniya don gaya musu su yi surutu don … mutanen da suka kama ni da iyalina”.

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa jami’an sojin Gabon sun sanar da kwace mulki bayan sake zaben Bongo karo na uku.