Kasuwanci

Halasci Ko Haramcin Kuɗin Crypto – Prof. Umar Sani Fagge

Assalamu alaikum wa rahmatullah

Prof. Umar Sani Fagge ne yayi tsokaci a cikin wani bidiyo da muka ci karo akan YouTube game da kuɗin cryptocurrency.

Hakika Mallam yayi maganganu masu taba zuciya kuma masu ma’ana. A cikin maganar da yayi ya bada ka’idoji guda uku da kasuwanci ke iya halasta, ma’ana idan ka cika wannan ka’idojin uku to abin da ka samu daga wannan kasuwancin halal ne, indai babu wani nassi karara da ya haramta abin da kake kasuwanci ba.

Na farko Maliam yace kana bukatar hannun jari, ma’ana (Capital) da zaka zuba domin juyawa da niyyar idan hajar ta kara daraja ka sayar ka samu fa’ida.

Na biyu Mallam yace kana bukatar ilimin gudanar da kasuwanci, wanda idan muka dauko wannan maganar zuwa crypto zamu iya kiran wannan da ilimin Analysis (Both Technical, Fundamental, On-chain and other related skills) a hada-hada.

Na uku mallam yace idan ka hada wadancan abubuwa biyu, sai kuma ka jira masu saya.

Malam yayi wannan maganar cikin minti dayan farko na bidiyon, wanda kuma hakan ya fito da masu tradit cryptocurrency na (Spot Trading) bisa ilimi cewa lallai halal suke ci, domin sun cika duka ka’idojin; suna saka kudin su a matsayin jari, sannnan sun bata lokaci shekara da shekaru muna neman ilimi har Allah ya musu muwafaka suka iya analysing ɗin kasuwa, su gane me ya kamata su saya, a ina ya kamata su saya sannan a ina ya kamata su sayar, sannan idan mukayi analysis sai su sayi coins da suke ganin za’a samu riba dasu, su rike su sannan du jira har lokacin da farashin su zai tashi kuma a samu masu saya su sayar musu a exchange (DEX ko CEX).

Bayan Mallam ya gama wannan bayanin sai ya tambayi almajiransa shin akwai wannan abubuwan guda uku? sai wasu suka ce babu, wanda hakan ya tabbatar da cewa lallai basu fahimci mene ne crypto trading ba da yadda yake gudana. Wannan amsa da aka baiwa malam sai ya dora akanta, cewa toh indai babu wancan abubuwa 3 toh lallai haram ne kuma bai halatta ba, har ya kawo misalai wanda suke nuna mallam ya danganta crypto da ponzi schemes da sauran damfara da ake yi da kuma get rich quick schemes.

Amma muka tsaya muka fahimci su almajiran, sai muka gane suna kokarin danganta lamarin da mining ne; wanda shi kuma mining ba trading bane, wani aiki kake yi ake biyan ka, wanda na tabbatar idan aka yiwa Malam bayaninsa shima, da yadda yake aiki tabbas malam bazai haramta shi ba.