Labarai
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAE Ta Aika Taimakon Magunguna Zuwa Masar Domin Gaza
Hadaddiyar Daular Larabawa ta aike da wani jirgin sama da ke dauke da agajin kayan jinya na gaggawa zuwa birnin Arish na kasar Masar domin shigar da shi zirin Gaza ta mashigar Rafah, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Emirates ya sanar a ranar Juma’a.
Bugu da kari, Sheikh Maktoum bin Mohammed bin Rashid Al Maktoum, mataimakin shugaban kasar Dubai na farko, mataimakin firaministan kasar kuma ministan kudi na Hadaddiyar Daular Larabawa, ya bada umarnin bayar da agajin jin kai dirhami miliyan 50 ga Falasdinu.
A cewar WAM, taimakon ya zo “a matsayin wani ɓangare na manufofin UAE don bada agajin gaggawa da taimako ga jama’a masu rauni da kuma masu bukata a duniya a lokutan rikici.”