Gangar Ɗanyen Mai Miliyan 107 Sun Ɓace Ƙarƙashin Gwamnatin Buhari A 2019

Gangar danyen mai fiye da miliyan 100 sun bace karkashin mulkin Buhari a shekarar 2019.

Kamfanin NNPC da yan majalisar shi suka gano badakalae yayin da suke nazarin wani rahoto daga babban mai binciken kudi na Najeriya..

A cewar rahotannin kafafen yada labarai na cikin gida a ranar Laraba, an gano sakamakon a kwanan baya a yayin wani zaman hadin gwiwa na kwamitocin kan asusun gwamnati a majalisun biyu, domin tantance rahoton.

A cikin rahoton, ofishin babban mai binciken kudi na gwamnatin tarayya ya zargi kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), da gazawa wajen yin bayani inda kusan ganga miliyan 107.2 na danyen mai da aka fito da su domin amfanin cikin gida a shekarar 2019.

“An bukaci Manajan Darakta na Kamfanin NNPC da ya samar da cikakken jadawalin rabon danyen mai ga matatun mai daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga Disamba, 2019, tare da bayar da cikakkun bayanai na sayar da danyen mai da ba a yi amfani da shi ba tare da daidaita shi da jimillar danyen mai na cikin gida. 107,239,436.00 bbls ya fita cikin 2019 kuma adadin da aka samu daga sayar da danyen mai da ba a yi amfani da shi ba ga Asusun Gwamnatin Tarayya, “inji rahoton.

Har ila yau, samu rarrabuwar lissafi a cikin kudaden da aka tura a asusun gwamnati, inda ya ce Akanta Janar na Tarayya yace Naira ₦608,710,292,773.44 ne kawai ya samu, duk da cewa NNPC tace ta mika Naira miliyan ₦1,272,606,864,000 ($3bn).

Mai magana da yawun NNPC bai amsa tambayoyi da yawa daga Al Jazeera ba.