Labarai

Ganduje Yaro Na Ne, Bai Iya Kallon Ido Na – Kwankwaso Yayi Martani Ga Barazanar Marin Sa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya mayar da martani kan barazanar da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ta marin sa a ranar Juma’a a fadar shugaban kasa ta Aso Rock.

Kwankwaso wanda yayi dariya a kan barazanar mari da aka yi da shi a wata hira da Sashen Hausa na BBC a ranar Asabar, ya ce Ganduje na cikin rudani lokacin da yayi wannan barazanar, kuma Kwankwaso yayi zargin cewa shi (Ganduje) “yaron” ne na siyasa da ba zai iya kallon idonsa ba balantana maganar marin sa.

Ganduje wanda yayi wannan barazanar ne biyo bayan rushewar da Gwamna Abba Kabiir Yusuf yayi a jihar wanda ya zarga da karbar umarni daga Kwankwaso, yace da ace ya gana da shi a Villa.

Jim kadan bayan ganawarsa da shugaba Tinubu, Ganduje ya amsa tambayar da ‘yan jarida suka yi masa:

“Na san yana cikin ginin amma ba mu hadu ba. Watakila idan muka hadu, watakila zan iya marin sa.”

Sai dai a hirar da yayi da BBC, Kwankwaso yace tabbas Ganduje ya rude a lokacin da ya bayyana hakan

“Na ji Ganduje ya ce da ya mare ni, amma ina nan. Ya rude kawai.

“Duk wadannan ’ya’yana ne a siyasance. Ba ya iya kallona kai tsaye idan muka hadu.

“Ya kasance cikin rudani lokacin da ya fadi haka, wadannan ‘ya’yan siyasa na idan sun gan ni sai su runtse idonsu,” in ji tsohon Gwamnan.