Kasuwanci

Farashin Buhun Siminti Zai Iya Kai N9,000 A Najeriya – Kamfanoni

Kungiyar masu har-hadawa da samar da siminti ta Nijeriya ta ja kunnen al’umma cewa muddin gwamnatin Tarayyar Najeriya ba tayi watsi da shirinta na amfani da tsarin aiki da siminti ba domin yin hanyoyin kankare a kan titunan da ake ginawa ba, to farashin siminti zai iya kai wa Naira N9,000 a kasar.

A halin da ake ciki dai, ana sayar da buhun simintin mai nauyin kilogram 50KG kan kudi N5,000 ko fiye a wasu sassan kasar.

Kazalika, kungiyar ta ja hankalin al’umma cewa akwai bukatar gwamnati ta sa baki wajen yawan tashin farashin da simintin ke yi a ‘yan kwanakin nan ta hanyar kai dauki a masana’antar sarrafa simintin.

Kungiyar a cikin wata sanarwa daga Shugabanta Prince David Iweta da Sakatare Reagan Ifomba, ta yaba wa ma’aikatar aikace-aikace ta tarayya da take kokarin yin amfani da simintin a wajen gine-ginen hanyoyi, sai dai ta ja kunnen cewa yawan amfani da simintin zai sa a rika nemansa a kai a kai da kuma hakan zai sa yayi tsada a kasuwa.