Labarai

Falasɗinawa Basu Da Niyyar Barin Ƙasar Su

Tamer Qarmout, farfesa kan manufofin jama’a a cibiyar nazarin karatun digiri na Doha, ya ce akwai bukatar a samar da mafita mai ɗorewa ga Falasdinu daba ta shafi tsammanin Falasɗinawa su bar ƙasarsu ba.

“Falasdinawa ba sa son barin gidajensu. Falasdinawa mutane ne masu girman ra’ayi, ”in ji Qarmout ga Al Jazeera.

“Falasdinu ita ce mahaifarsu. Su ’yan asalin ƙasar ne kuma ba su cancanci wannan ba. Ba sa son zama ‘yan gudun hijira a wata kasa,” in ji shi.