Labarai

Duniya Ta Mayar Da Martani Kan Girgizar Kasar Maroko Da Ta Kashe Mutane Aƙalla 2,000

Bayan girgizar kasa mai karfin awo 6.8 da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,012 tare da jikkata wasu 2,059 yayin da kuma ta rusa gidajen su, hukumomi a ranar Asabar din da ta gabata sun ayyana kwanaki uku na zaman makoki na kasa.

Martani daga al’ummomin duniya, yayin da labarin bala’in girgizar kasar ta Maroko ke yaduwa.

Turkiyya na cikin kasashen da ke nuna goyon baya tare da bayar da goyon baya bayan girgizar kasa mai karfi a cikin watan Fabreru da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 50,000.

Aljeriya wacce ta yanke hulda da kasar Maroko a shekarar 2021 sakamakon tashin rikicin da kasashen biyu ke yi kan batun yankin yammacin sahara, ta sanar da cewa za ta bar jiragen jin kai da na magunguna su yi shawagi a sararin samaniyarta.

Duk da cewa an sami tayin taimako da yawa daga ko’ina cikin duniya, gwamnatin Moroko ba ta nemi taimako a hukumance ba, wanda ake bukata kafin ma’aikatan ceto na waje su isa.