Kasuwanci

Dangote Ya Rasa Matsayin Shi Na Wanda Yafi Kowa Kuɗi A Afrika

Aliko Dangote ya yi asarar kambun mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka a hannun hamshakin attajiri dan kasar Afrika ta Kudu, Johann Rupert.

A cewar Forbes Billionaire Ranking da aka gani a ranar Lahadi, dukiyar Dangote ta ragu da kashi 20.7 cikin dari a cikin rage darajar Naira da babban bankin Najeriya (CBN) ya aiwatar.

CBN ya rage darajar Naira, lamarin da yasa darajar kudin Najeriya ta ragu da kashi 40.5 cikin 100 tun bayan faduwar darajar Naira a makon jiya Laraba.