Labarai

Boko Haram Ta Sha Alwashin Sake Kwato Garuruwan Da Jami’an Tsaro Suka Karba

Kungiyar Boko Haram da aka fi sani da Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād ta sha alwashin kwato yankunan da sojojin Najeriya suka kwato.

Wani faifan bidiyo da aka yada a kan X, wanda wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma kwararre kan yaki da tada kayar baya a tafkin Chadi, Zagazola Makama, a ranar Lahadi.

‘Yan ta’addan sun kuma yi barazanar kai hari ga Civilian Joint Task Force (CJTF) da ake kira ‘Yan Red Cross.

‘Yan ta’addan sun zarge su da hada karfi da karfe da sojoji domin kai musu hari a yankunansu.

Daya daga cikin ‘yan ta’addan da ke magana da harshen Hausa a cikin faifan bidiyon, ya ce, “Mun zo nan ne domin mu sanar da mu da babbar murya cewa mun dawo kuma mun dawo gaba daya domin kwato dukkan yankunan da muka rasa a hannunku (kafirai).

“A gare ku Red Cross, kun yi murna saboda sun ba mu makamai; ka sani cewa karya ce, ba za ka yi nasara a kan Musulunci ba. Mun dogara da ikon Allah kuma da ikonsa za mu yi nasara”.