Labarai

Bala Lau, Kabiru Gombe Sun Gana Da Gwamnan Bauchi Kan Dr. Abdul-Aziz Idri

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya jagoranci tawagar Jigajigan Malam Addini Musulunci na ƙasar nan sun ziyarci gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad domin tattaunawa kan yadda za’a kawo karshen taƙaddamar da ta sanya kotu ta tsare Dutsen Tanshi Dr. Idris Abdul’aziz.

Tattaunawar wacce ta ƙunshi shugaban kungiyar Izala ta ƙasa Sheikh Bala Lau, sakataren Kungiyar Sheikh Kabiru Haruna Gombe, Sheikh Abdulwahab na Kano da shugabannin ɓangarorin kungiyoyin Addini Musulunci na jihar Bauchi da sauran Masu ruwa da tsaki kan taƙaddamar sun sami kyakkyawan fahimta kan yadda lamarin zai zama tarihi.

Da yake jawabi Gwamna Bala Abdulƙadir yace yadda aka zauna aka tattaunawa akaji ta bakin ko wani ɓangare shine Adalci ba wai kawai yadda wasu malamai ke hawa mimbari suna ta zage zage da maganganun da basu dace ba sakamakon rashin bincike kan haƙiƙanin abinda yake faruwa ba.

Sai yayi godiya wa gwamnan da malaman bisa ɗaukar wannan matakin jin tabakin ko wani ɓangare, yana mai cewa da yadda Allah komai ya kawo karshe.

Shima cikin jawabinshi gwamnan jihar Adamawa Rt Hon Ahmadu Umaru Fintiri yayi godiya ne bisa dama da gwamnan jihar Bauchi ya basu suka tattauna kan lamarin kuma har aka sami maslaha.

Ofishin Mukthar Gidado mai baiwa Gwamnan jihar Bauchi shawara kan harkokin yada Labarai
28/July /2023.